A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Talata ma’aikatar tsaron kasar Irakin ta ce an jibge dakarun kasar a wasu yankuna guda biyar da ke kusa da garin na Musil da nufin kaddamar da wani hari na gaba daya don ‘yanto garin daga hannun ‘yan ta’addan na Da’esh da kuma sauran gyauron ‘yan jam’iyyar Ba’ath.
Cikin ‘yan kwanakin nan dai sojojin Irakin da suke samun daukin al’ummar kasar sun kaddamar da wasu sabbin hare-hare kan yankunan da ‘yan ta’addan suka mamaye inda suka sami nasarar hallaka wani adadi mai yawa da kuma kwace wasu yankuna da a da suke hannun ‘yan ta’addan.
A bangare guda kuma ma’aikatar tsaron kasar Irakin ta sanar da shirin fara amfani da jiragen yakin da ta sayo daga kasar Rasha wadanda kuma wasunsu suka fara isowa za su fara wajen kai hare-hare kan ‘yan kungiyar ta ISIS da ake ganin zai iya sauya yanayin fada da ‘yan ta’addan.ABNA